6 Satumba 2024 - 10:15
Hizbullah Ta Kai Hare-Hare Kan Barikin "Ramut Naftali" Na Sojojin Yahudawa

Hare-haren da mayakan Hizbullah suka kai a barikin "Ramut Naftali" na sojojin yahudawan sahyoniya ya kara tsanani.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA - ya kawo maku rahotone cewa: A cikin wata sanarwa da kungiyar ta Hizbullah ta fitar ta sanar da cewa, ta aiwatar da wani harin makami mai linzami da jiragen sama mara matuki kan barikin Ramot Naftali da ke arewacin kasar Falasdinu da yahudawan sahyuniya suka mamaye.

A cewar wannan sanarwa, yazo cewa wannan farmaki na mayakan Hizbullah na kasar Labanon ya faru ne a matsayin mayar da martani ga ci gaba da laifukan da gwamnatin sahyoniya ta ke yi a kan iyakokin kudancin kasar ta Lebanon.